Friday, 10 August 2018

Tsananin zafi ya kashe mutane 138 a Japan

Ya zuwa mutane 138 ne suka mutu sakamakon tsananin zafi da ke addabar jama'ar kasar Japan wanda aka fara watanni 3 da suka gabata.

Rahoton da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta japan ta fitar na cewa, a watanni 3 da suka gabata mutane dubu 71,266 ne suka kai kansu asibiti sakamakon kamu wa da cututtuka da suke da alaka da zafin rana.

Rahoton ya ce, a wannan karon an fuskanci zafin da ba a taba gani a kasar ba a cikin shekaru 40.

A shekarar 2013 ma an yi tsananin zafi a Japan.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment