Friday, 10 August 2018

Tsananin zafi ya salwantar da rayuka a Koriya ta Kudu

An bayyana cewa tsananin zafi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42 a Koriya ta Kudu.


Jaridar "South China Morning Post" ta rawaito cewar a ƙarshen watan Mayu tsananin zafin da ba'a taba irisai ba cikin shekaru 111 a ƙasar ya salwantar da rayuka 42.

Darajar zafin da yakai 40 ya sanya kwantar da mutane dubu 3 da 500 a asibiti.

Gwamnatin kasar ta rage kuɗaɗen wutar lantarki domin aji sauƙin amfani da na'urori masu sanyaya ɗakuna.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment