Thursday, 16 August 2018

Tura ta kai bango: Anyi artabu tsakanin jama’an gari da yan ta’addan jihar Zamfara

Dama dai masu iya magana na cewa idan tura ta kai bango komai zai iya faruwa, hakan ne ta tabbata akan jama’an wani kauye mai suna Yanware dake cikin karamar hukumar Tsafe inda suka fafata da yan bindiga, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Wannan lamari ya faru ne a daren Laraba, 15 ga watan Agusta, lokacin da wasu gungun yan bindiga suka yi kokarin afkawa cikin kauyen don yin ta’addanci tare da satar duk abinda suka gani.

Sai dai dayake lokacin sallar Isha’I ne yan bindigan suka yi kokarin afkawa kauyen, don haka babu jama’a sosai a waje, musamman maza, sai yan kadan, amma duk da haka sai da wadanda suke waje suka tari yan bindigan har saida suka samu dauki daga sauran jama’an da suka dawo daga Masallaci.

A haka dai aka dinga musayar wuta tsakanin yan bindigan da jama’an kauyen, ana ta barin wuta kowa na neman sa’ar kowa, har sai da yan bindigan suka fahimci anfi karinsu, kuma ba tare da wata wata ba suka ranta ana kare.

Rahotanni sun bayyana an samu wadanda suka jikkata daga dukkanin bangarorin biyu, sai dai babu wani tabbataccen rahoto game da adadin wadanda suka jikkatan ko suka mutu, wannan yasa jama’an yankin ke kira ga Dakarun Soji dasu kawo musu dauki don gudun harin ramuwa daga yan bindigan.
Naija.ng

No comments:

Post a Comment