Sunday, 5 August 2018

UAE ta saye kamfanin kera makamai na Faransa

Hadaddiyar Daular Larabawa ta saye kamfanin kera makamai na Manurhin na kasar Faransa.


Kafar yada labarai ta France 24 ta rawaito cewa, kamfanoni uku wadanda suka hada da Odyssée Technologies na Faransa,New Lachaussée na Belgium da Delta Defence nakasar Slovakia ne suka nuna bukatarsu ta  sayen Manurhin wanda ya kwashe shekaru da dama yana fama matsolin kudi, amma kwamitin cinikaiya ta kotun birnin Mulhouse ta yanke hukuncin sayar wa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), saboda ta dauki alkawarin rike sama kashi 2 cikin 3 na ma'aikatan da kamfanin ke da shi.

Manurhin ta fara aiki karkashin jagorancin kamfanin tsaro ta UAE, Edic a ranar Larabar nan da ta gabata.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment