Thursday, 23 August 2018

UWAR GIDAN SHUGABAN KASA TA ZIYARCI MARASA LAFIYA A DAURA

Da Yammacin jiya Laraba ne Uwar gidan Shugaban kasa Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta kai Ziyara ta Musamman tare da dubiya ga Marassa Lafiya a Babban Asibitin garin Daura (General Hospital) na Sabon ginin da ta gina na Bangaren Mata da yara inda ta duba su tare da Yi musu Barka da Babbar Sallah, daga karshe kuma ta basu Gudummawa domin Kyautatawa tare da jin kai.Uwar Gidan Shugaban kasar tayi matukar farin ciki sosai da ganin cewa Sabon wajen da ta gina a Asibitin Al'umma suna amfanuwa da shi yadda ya kamata.

A Yayin Ziyarar ta samu Rakiyar Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zakiyya Masari tare da sauran yan Tawagarta.

Hotuna:📸Haye C. Okoh

No comments:

Post a Comment