Sunday, 5 August 2018

Wanda suka yi garkuwa da Sheikh Algarkawi sun sakoshi

Rahotanni sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutane da suka sace shahararren malamin addinin nan na Kaduna, Sheikh Ahamad Adam Algarkawi sun sakoshi.


Saidai babu cikakken bayani akan ko an biya kudin fansa ko kuwa a'a.

Sheikh Algarkawi yana zaunene a unguwar Kinkinau dake Kaduna, yana da Makaranta da Masallaci me hawa biyu da kuma asibiti dake karkashinshi.

Malamin yayi suna sosai wajan kwatanta zuhudu, watau gudun Duniya.

A ranar Alhamis din data gabata ne aka sace malamin tare da wasu dalibanshi bayan da sukaje gona.

Jama'ar gari sun rika rade-radin cewa wasu makudan kudine da malamin ya gada daga gurin wani attajirin dalibinshi daya rasu suka sa aka yi garkuwar dashi.

No comments:

Post a Comment