Tuesday, 28 August 2018

Wani dan takarar shugaban kasa yayi alkawarin barin 'yan Madigo da Luwadi su wataya idan yaci zabe

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara karatowa, 'yan siyasa na ta yin alkawuran da suke ganin zasu ja ra'ayoyin 'yan Najeriya domin su zabesu, saidai Alkawarin da me neman takarar shugabancin kasarnan wanda tsohon gwamnan Rivers ne yayi, Donald Duke ya bar mutane cikin mamaki da haushi.


Shidai Donald ya bayyanawa manema labarai cewa, matsalar Najeriya shine rashin shugabanci na gari.

Yace gaba da cewa, bai san yanda 'yan Luwadi da madigo ke ji ba da suke sha'awar jinsin halittarsu ba amma abinda zai tabbatar shine idan ya zama shugaban kasa zai basu kariyar da doka ta tanada.

Ya kara da cewa, zai ma iya nada dan luwadi ko 'yar Madigo mukami a gwamnatinshi kawai dai shi fatanshi ya zamana zai iya yin aikin da aka bashi.

Saidai da dama da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan batu sunce gaskiya ya basu kunya da wannan kalamai suka fito daga bakinshi, kuma ya fado kasa warwas dan ba zasu zabeshi ba.

No comments:

Post a Comment