Wednesday, 29 August 2018

Wani matashi ya yi barazanar kashe kan sa idan Buhari na ci zabe ba


Wani matashi a Abuja ya ja hankalin jama’a a Abuja bayan ya bayyana cewar zai kasha kan sa matukar shugaba Buhari bai ci zaben 2019 ba.


An hangi matashin wanda bai wuce shekarar 30 ba a unguwar Garki ta Abuja dauke da wata babbar fosta dake dauke da sakon zai kasha kansa idan Buhari ya fadi zabe a 2019.

Wata masoyiyar shugaba Buhari, Hadiza Bagudu, da ta yada hoton ta bayyana cewar ba zata iya kasha kanta saboda Buhari ba.

“Ina tafiya a unguwar Garki, Abuja, na ga wannan matashi dauke da fosta da rubutun cewar zai kasha kansa idan Buhari bai ci zaben 2019 ba,” kamar yadda Bagudu ta rubuta a shafinta na Facebook.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment