Thursday, 23 August 2018

Wani mutum ya jawo hankulan kafofin watsa labarai na Duniya da kungiyoyin kare hakkin dabbobi wai akan yanda shugaba Buhari ya yanka ragon Sallah

Wannan mutumin ya bayyana rashin jin dadinshi akan yanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yanka ragon layyarshi inda yayi kira ga kafafen watsa labarai na Duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin dabbobi da su zo suga yanda Buharin ya yanka rago.Mutumin ya kawo wasu salwantar rayuka da aka samu a baya wanda yace shugaba Buharin be tanka a kai ba.

Wannan lamari ya dauki hankulan mutane a shafin Twitter inda a nanne mutumin yayi wannan magana inda da dama suka sokeshi akan wannan lamari.

1 comment:

  1. Wannan mutumin wawa ne kuma sakare,saboda baya da fahimta a rayuwarsa kwata-kwata.

    ReplyDelete