Wednesday, 8 August 2018

Wasu tsofaffi 2 sun gudu daga gidan da ake kula da su zuwa wajen Chasu

Wasu tsofaffi 2 A kasar Jamus sun gudu daga gidan kula da gajiyayyu da ake kula da su tare da halartar taron kida da rawa na Open Air wanda daya daga cikin wasannin chasu mafiya girma ne a Turai.


Gidan rediyon NDR na Jamus na sanar da cewa, 'yan sandan sun gano tsaffin mutanen ma'aurata sun gudu daga gidan kula da gajiyayyu sai suka bi bayansu zuwa wajen rawar tare da samunsu cikin nishadi.

Labaran sun ce,  Akwai mawaka irin su Judas Priest, Red Hot Chili Peppers da In Flame a wajen chasun inda suka sanya tsofaffin kin koma wa gidan gajiyayyun.

'Yan sanda dole suka hakura tare da koma wa da motar tasin da aka aika zuwa wajen daga gidan ajje gajiyayyun.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment