Friday, 3 August 2018

Wata duniya ta matso kurkusa da tamu duniyar

Duniyar Mars ta sakko kurkusa da tamu duniyar wanda wannan ce kusantowa mafi girma a cikin shekaru 15 da suka gabata.


Labaran da shafin yanar gizo na "Space.com" ya fitar na cewa, duniyar ja ta zo kusa da tamu da nisan kilomita miliyan 57.6 wanda shi ne mafi kusantowa tun shekarar 2003.

A tsarin motsawar rana duniyar Mars ce ta 4 mafi kusanci da rana inda ta ke da nisan kilomita miliyan 230 daga ranar.

Ana kammala zagaya duniyar rana a cikin kwanaki 365 amma ita kuma Mars ana kammala tata a cikin kwanaki 687.

Idan har duniyar Mars za ta zo kusa da tamu duniyar to dole ne sai ta fara kusantar rana.

A shekarar 2003 duniyar Mars ta zo kusa da duniyarmu da n,san kilomita miliyan 55.6.

Ana sa ran sake kusantowar ta a shekarar 2287.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment