Friday, 10 August 2018

Watakil DSS su sako Dasuki, Zakzaki da wadanda aka tsare ba bisa ka'idar kotu ba

Akwai yuwuwar mai bada shawara ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan akan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, ya samu sassauci bayan tsare shi da akayi na shekaru biyu a karkashin mukaddashin shugaban jami'an yan sandan farin kaya, Matthew Seyifa.


Seyifa da ya tattauna da kafafen yada labarai a ofishin dake Abuja a yau, ya bayyana cewa hukumar zata duba wadanda aka kama kuma aka tsare bayan ta samu bayanin da ya dace daga wadanda abin ya shafa.

Duk da dai bai fadi yaushe zasu saki Dasuki ba, Seyifa ya tabbatar da cewa duk matsalolin kame ba tare d ka'ida ba da tsarewa da hukumar tayi ana kan kara duba su domin tabbatar da cewa babu Dan kasa da aka tsare ba tare da bin ka'idoji ba.

Seyifa yace "Ana min bayani akan Dasuki. Zaku iya kara jin ta bakina bayan na gama sauraron bayanin. Nan da kwanaki kadan zamu kara duba duk al'amuran, balle wanda ya jibanci DSS da sauran hukumomi da suke aiki tare damu don karfafa tsaro."
Naija.ng

No comments:

Post a Comment