Sunday, 5 August 2018

Wulakanci da rashin ganin girmanshi da gwamnan Kano keyi yasa mataimakin gwamnan jihar ya ajiye mukaminshi

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya ajiye mukaminshi inda ya bayyana cewa, rikicin da yaki ci ya ki cinyewane dalilin daukar wannan mataki nashi.


Farfesa Hafiz ya bayyana hakane a cikin wata takarda daya aikewa gwamnan jiya, Asabar inda ya rubuta a ciki cewa, yayi ta jawo hankalin gwamna akan rikice-rikice dake faruwa yanzu amma gwamnan yaki daukar wani mataki akai.

Ya kara da cewa gwamnan ya rika wulakantashi da kuma ofishinshi na mataimakin gwamna inda yayi hakuri da hakan har na tsawon shekaru biyu da rabi amma yanzu kam tazo karshe.

Koda a makon daya gabata sai da Farfesa Hafiz ya bayyanawa BBChausa a wata hira da sukayi dashi cewa gwamnan Kanon yana gasa mishi aya a hannu.

No comments:

Post a Comment