Sunday, 12 August 2018

Wutar dajin dake ci a Amurka fushin Allah ne saboda ayyukan luwadi da madigo>>Inji wani faston kasar

Wani fasto a California da ke Amurka ya zargi 'yan Luwadi da madigo zama ummal aba'isar mahaukaciyar gobarar da ke ci gaba da lakwame jiharsu.


Malamin cocin mai suna Kevin Swanson ya jaddada cewa,ubangiji na yin fushi da su,sabili da yadda gwamnatin Amurka ta rufe idanu kan aika-aikan 'yan Luwadi da Madigo,inji jaridar The Independent.

Swanson ya ce, "A shekarar 2005 an yi na'am da dokar auren jinsi daya,amma a shekarar 2008 aka yi watsi da ita.A shekarar 2017 kuma, a dinka da'awar yada wannan mguwar akidar a makarantun gwamnati.Tun a lokacin ne gobara ta fara kunno kai a California.Abinda za a yi la'akari da shi a nan shi ne, Allah na ci gaba da kone jihar tun shekarar 2017 ya zuwa yau.

A yanzu haka, jihar na da wakiliyarta ta farko, ma'abociyar madigo,Toni Atkins a majalisar dattijan Amurka.

Masana kan ilimin yanayi na Amurka sun yi watsi da wannan furucin na faston,inda suka ce lamarin na da nasaba ne da dumamar yanayi kawai.

A baya ma, Swanson ya sanar da cewa, mawakiya Lady Gaga na da aljanu.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment