Saturday, 4 August 2018

Yadda awaki suka mamaye unguwanni a Amurka

Fiye da awaki 100 ne suka mamaye titunan yankin Boise a jihar Idaho da ke kasar Amurka, lamarin da ba a saba gani ba a kasar.


Awakin sun balle ne daga garkensu a ranar juma'a, inda suka shiga gari suna neman abinci.

Awakin sun ja hankalin mazauna Boise inda aka wayi gari da awakin suna kiwo a cikin gari.

An ta yada hutuna da bidiyon awakin a kafafen sada zumunta na Intanet.

Wani a shafin twitter ya ce bayan shekara 30 za su ba jikokinsu labarin yadda awaki suka tsere daga garkensu suka shigo gari.

Rahotanni sun ce awakin sun balle ne da misalin karfe bakwai na safe daga garkensu bayan wadanda ke kiyonsu sun tafi gyaran wani filin kiwo.

Yara da manya a unguwarsun fito suna ta wasa da awakin, abin da ba su taba gani ba a gidajensu.
BBChausa

No comments:

Post a Comment