Tuesday, 7 August 2018

Yadda girgizar kasa ta riske mutane a masallaci a Indonesiya

Wani masallaci da ya rushe a Pemenang, Arewacin Lombok ran 6 ga watan Agusta, 2018
Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutane a buraguzan masallacin da ya rushe a tsibirin Lombok da ke kasar Indonesiya, bisa fargabar da ake yi cewa akwai wasu mutane da suka makale a ranar Lahadi bayan da akai girgizar kasa.


Girgizar kasa da ta kai maki 6.7 ta kashe kusan mutum 100 kuma ta sa mutane 20,000 sun rasa matsugunansu.
Masallacin na daya daga cikin dubban gine-ginen da suka ruguje a arewacin Lombok.
Hukumar ceto ta Indonesiya ta ce an ceto mutum biyu daga cikin baraguzan ginin.
Girgizar kasar ta faru ne ranar Lahadi lokacin da ake sallar Isha.
Wani ganau ya sahida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa a lokacin akwai kusan mutum 50 a cikin masallacin Jabal Nur da ke nan kauyen Lading-Lading.
Kelana dan shekara 53 ya ce Limaminsu ya gudu ana sallah sai sauran mamu ma suka bi shi.
An samo gawarwaki guda uku da suka rudiddige a cikin baraguzan masallacin.
Mai magana da yawun hukumar ceto Sutopo Purwo Nugroho, ya ce an tsinci takalma da yawa a kofar masallacin, hakan ya sa ake tsoron ko za a samu wasu gawarwakin.
Ya yada hoton bidiyon wani mutum ana ciro shi daga karkashin 'baraguzan gine-gine.
Tsibirin Lombok ya kai kimanin murabba'in kilomita 4,500 wanda yake gabashin Tsibirin Bali.
Tasirin girgizar kasar da aka yi wannan Lahadin ya fi wanda akai a Lombok makon da ya gabata inda mutane 16 suka rasa rayukansu.
Hukumomi sun ce wadanda suka mutu sun kai 98 amma jami'ai sun yi amanna cewa adadin na iya karuwa. Galibin mutanen sun rasa rayukansu ne bayan da baraguzan gini ya fado musu.
Masu ceto sun ce yanzu abin da ya fi masu muhimmanci shi ne su samar wa marasa matsuguni wurin zama, saboda har yanzu fargaba ba ta saki mutanen da ke wajen ba.
A babban birnin Lombok Mataram, ma'aikatan asibiti na kokarin ganin sun kula da wadanda suka ji rauni a asibitocin da suka rushe. Sun koma kula da mutane a waje.
Amma kungiyar agaji ta Red Cross ta ce akwai wani abun al'ajabi da ya faru a lokacin ibtila'in.
Ma'aikatan kungiyar sun tainakawa wata mata mai shekara 38 ta haihu a wata cibiyar kula da marasa lafiya ta wucin gadi a ranar Litinin.
Daya daga cikin sunayen da matar ta sanyawa 'yar tata shi ne "Gempa" wanda yake nufin girgizar kasa a yaren Indonesiya.
A lokacin da girgizar kasar ta auku Philipa Hodge na Otal din Katamaran da ke nan arewacin Mataram. Ta fadawa BBC cewa wuta ta dauke sai kuma aka shiga rudani a wajen.
"Mutane na ta turereniya don su samu su fita a wurin, kuma gilasai suka farfashe. Sai muka ji baraguzai na fado mana.
Ban ga saurayina ba amma ina ta kiran sunansa. Daga baya dai sai muka ga juna kuma akwai jini a fuskarsa da rigarsa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment