Thursday, 23 August 2018

Yadda Hawan Daushe Ya Gudana A Jihar Kano

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll, ya gudanar da hawan daushen kamar yadda aka saba daya ga babbar sallah, kuma an gudanar da shi ne a kan "Taguwa" wato rakuma kamar yadda aka saba yi duk shekara. Sarki ya yi wannan hawan ne tare da hakiman sa da masu ruwa da tsaki na masarautar Kano.Hawan Daushe na bana ya samu halartar mai girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da Sanata Barau I Jibril, Sanata Kabiru Gaya, Sakataren Gwamnati Malam Usman Alhaji da Dan Majalisar Jiha Baffa Babba Dan Agundi da 'yanmajalisu, kwamishinoni, shugaban jamiyyar APC Alh. Abdullahi Abbas da sauran jami'an gwamnatin Kano da sauran manyan baki daga ciki da wajan jihar Kano dama Najeriya baki daya.

A tsarin yadda hawan daushen ke gudana, bayan ya bi wasu sassa na cikin birni an gaisa da al'umma sai ya shiga unguwar Gwangwazo zuwa gidan mai babban daki ya yi gaisuwa da sanyawa rayuwarsa albarka idan ya fito Sarki ya kan tsaya inda hakimai tare da mahaya dawaki suke sukuwa wanda ake kira "Jayi" domin kawo gaisuwa da dafi ga mai martaba sarki. Sannan sai a jera bindugu kusan guda 30 suna tashi da kansu. Bayan Sarki ya karbi gaisuwa, masu hawa sun gama abubuwan da aka saba na al'ada, daga bisani sai Sarki ya koma cikin gida ta kofar kudu. Sakamakon irin yadda Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll, yake gudanar da salon mulkinsa cikin adalci, tallafawa marayu da gajiyayyu tare da taimakawa talakawa ta fuskokin rayuwa daban-daban, ya samu kyakkyawar tarba da kuma jinjina daga al'ummar jihar Kano, birni da kauye, da ma sauran sassan jihohi makwafta da suka halarci bukin na hawan daushe.

Kuma an yi wannan lami lafiya domin akwai tsauraran matakan tsaro, inda hadin gwiwar jami'an 'yan sanda masu kaki tare da na farin kaya da 'yan Hisba, 'yan Karota da sauran kungiyoyin samar da tsaro ga al'umma suka ba da gagarumar gudunmawa a wajen taron. 

Barka da sauka mai martaba Sarki Allah ya maimaita mana.
Rariya.

No comments:

Post a Comment