Saturday, 11 August 2018

Yadda na kubuta daga masu safarar mutane zuwa kasar Saudiyya, bayan dandana azaba da na yi

Wata daga cikin wadanda aka ceto daga kasar ta bayyan yadda ta fada tarkon masu yin safarar mutane har ta sami kanta a kasar Saudiyya.


Ta fara da cewa:

” Wata kawata ce ta hada ni da wata mata da ga dukkan alamu ejen ne irin masu shiryawa da nemo mutane domin safar su zuwa kasashen waje. Ita kanta kawata din ce mini ta yi wai tana zama ne a Dubai.

” Daga nan sai ta umarceni da in zo Abuja domin mu hadu da matan, domin ni a Legas nike zama.

” Bayan mun hadu sai aka kaini wani Asibiti a ka yi mini gwaje-gwaje. Daga nan sai matan tace mini za a kai ni kasar Saudiyya domin yin aiki. Ta ce min za a dinga biya na naira 150,000 duk wata.

” Aka yi mini takardun tafiya. Muna isa kasar Saudiyya sai komai ya canza. Na kare ne dai a akin wanke-wanke da shara, sannan suka kwace mini fasfo di na.

” Da wahalar ta yi yawa sai na kira ejen din, na gaya mata halin da nake ciki. Sai tace dole fa sai na ci gaba da zama a wannan wuri da nake aiki domin sai na yi aikin Naira Miliyan 1.7 tukuna kafin in bar gidan. Idan ba haka ba kuwa sai fa nayi aikin shekara biyu kafin a dawo dani gida.

” A haka ne fa na samu na kira wani abokina dan jarida shi kuma ya taimaka mini ya hada ni da NAPTIP, su kuma suka tuntubi ofishin jakadancin Najeriya dake Saudiyya har Allah yayi na kubuta daga hannun wadannan mutane.

Ta roki gwamnati da ta karkato akalar ta zuwa kasar Saudiyya domin kuwa akwai dubban matasa ‘yan Najeriya da aka yi safarar su zuwa kasar suna aikin bauta a can.
Premiumtimeshausa.

No comments:

Post a Comment