Friday, 10 August 2018

'Yan gida daya na takarar kujerar sanatan yankin Daura

Wasu 'yan uwa biyu wa da kaninsa za su fafata a zaben neman kujerar sanatan yankin Daura da ke jihar Katsina a Najeriya da za a yi ranar Asabar.


Ahmad Babba Kaita na jam'iyyar APC da dan uwansa Kabir Babba Kaita na jam'iyyar PDP ne 'yan takarar da suke fafatawa a wannan zaben a mazabar sanata ta arewacin Katsina wanda aka fi sani da yankin Daura.

Kabir wan Ahmad ne domin mahaifinsu daya ne daga garin Kankiya na jihar Katsina.
Ahmad shi ne dan majalisar mai wakiltar mazabar Kankia/Ingawa/Kusada a majalisar wakilan Najeriya.

Shi kuwa Kabir tsohon ma'aikacin hukumar hana fasa kwaurin kayayyaki ne wato kwastam.

'Yan uwan biyu na neman cike gurbin marigayi Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu a farkon watan Afrilun bana.

Wani abin sha'awa shi ne duk wanda ya yi nasara a zaben na gobe zai kasance wakilin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, domin garin Daura na cikin yankin Katsina ta arewa ne.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment