Friday, 3 August 2018

'Yan siyasa 3 da suka fi yawan canja jam'iyyu a Najeriya

Yayin da ake cikin wani lokaci da ‘Yan siyasa su ke ta fama sauya-sheka, mun kawo maku jerin wasu manyan ‘Yan siyasa da su kayi kaurin suna wajen canja Jam’iyya. Daga cikin wadanda su ka yi fice akwai Atiku Abubakar.


Ga dai jerin fitattun ‘Yan siyasan da aka san su da sake Jam’iyya:

1. Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya fara siyasa ne da dadewa inda ya nemi takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar SDP a 1993. Bayan nan sai a 1998 aka sake jin labarin Atiku inda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Adamawa a PDP. Atiku ya zama Mataimakin Shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda bayan nan kuma ya bar PDP yayi takarar Shugaban kasa a karkashin ACN a 2007. Daga baya kuma Atiku ya bar ACN ya dawo PDP inda ya sake takara a 2011. Atiku ya bar PDP a 2014 ya koma Jam’iyyar APC wanda ta karbe Gwamnati. A bara kuma Atiku ya sake barin APC ya dawo Jam’iyyar PDP.

2. Attahiru Dalhatu Bafarawa

Tsohon Gwamnan Sokoto Dalhatu Bafarawa ya fara siyasa tun a 1978 lokacin da yayi takara a karkashin Jam’iyyar GNPP amma bai kai labari ba. Da su Bafarawa aka kafa Jam’iyyar UNCP. Bayan nan Bafarawa yayi takarar Gwamna a 1999 a karkashin ANPP. Bayan Bafarawa ya Gwamna ya koma ya kafa Jam’iyyar DPP a 2007. Bafarawa ya bar DPP ya dawo ANPP. A 2014 Bafarawa ya shiga APC sai dai bai dade ba ya fice ya koma PDP daga karshe.

3. Aminu Waziri Tambuwal

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Aminu Tambuwal wanda ya bar APC kwanan nan yana cikin wadanda su ka fi kowa yawo. Tambuwal ya fara aiki ne da wani Sanata kafin ya zama ‘Dan Majalisa a 2003 karkashin ANPP. Daf da zaben 2007 sai Tambuwal ya koma Jam’iyyar DPP. Kafin a je ko ina Tambuwal ya koma Jam’iyyar PDP. A 2011 ya zama Shugaban Majalisa wanda kuma yayi bore ya bar PDP a 2014. Tamuwal ya zama Gwamna ne a tutar APC a 2015, yanzu haka Gwamnan na Sokoto yayi ficewar sa daga APC zuwa Jam’iyyar PDP.


No comments:

Post a Comment