Friday, 17 August 2018

Yanda mahaifiyata ta biyamin kudin makaranta da tallar Kifi

Soyayyar uwa da da ta dabance, babu abinda mutum zaiyi ya biya iyayenshi irin hidimar da suka mishi a rayuwa, to saidai kamar yanda yatsunmu suke, wani yafi wani tsawo, haka ita rayuwar da samun kowa da daidai nashi. Wata 'yar bautar kasace ta bayyana irin yanda mahaifiyarta ta biya mata kudin makaranta da sana'ar tallar kifi.


Irin wannan sadaukarwa da mahaifiyartata ta mata da kuma yanda itama take nuna mahaifiyartata da alfahari da ita ya matukar burge mutane a shafukan sada zumunta da muhawara.

Jama'a sun ta yi ma uwar da diyarta fatan Alheri.

Ga abinda tace akan mahaifiyartata:


 "Ina matu'kar son iyayena. Mamata ta ɗauki nauyin karatuna har na kammala jami'a da sana'ar sayar da kifi. Mamata nan ba da jimawa ba zan inganta rayuwarki. Ina matukar son ki mamata da babu kamarta a duk faɗin duniya."


No comments:

Post a Comment