Monday, 20 August 2018

Yanda Ronaldo yayi rugu-rugu da hancin wani Gola

A wasan da Juventus ta buga da kungiyar Chievo ranar Asabar din data gabata wanda ya kare Juve na cin Chievo din 3-2, Cristiano Ronaldo da golan Chievo din, Stefano Sorrentino sunyi wata taho mu gama da ta bar golan da karyayyen hanci.Bayan karon da golan yayi da Ronaldo, ya samu karayar hanci da kuma gurjewa a kafadarshi da ciwo a wuya, dole sai canjashi akayi aka sako wani golan. Daren wannan yinin a asibiti ya kwana, kamar yanda ESPN ta ruwaito.
Koda yake matar golan ta bayyana cewa bata son Ronaldo bayan da ya wa mijin nata illa, amma shi ya fito ta shafinshi ta yanar gizo ya bayyana cewa, ya godewa Ronaldo saboda ya aikemai da sakon Allah kyauta ya kuma bashi sauki.


No comments:

Post a Comment