Saturday, 11 August 2018

'Yar shekara 17 Ta yanke al-aurar saurayinta da wuka

Wata budurwa mai shekaru akalla 17 a duniya da ta fito daga karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa mai suna Ramlatu Tafida a shiga kanun labarai bayan da ta sa wuka ta yanke azzakarin saurayin ta.

Kamar dai yadda muka samu, saurayin nata mai suna Abdullahi Sabo dake da shekaru 25 a duniya yanzu haka yana kwance a asibitin Malam Aminu Kano yan karbar kulawa.

Koda yake dai kawo yanzu ba mu samu wani cikakken bayani ba game da dalilin da yasa budurwar ta aikata hakan, amma dai mun samu cewa tuni har an makata kotu.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment