Sunday, 5 August 2018

Yarima Salman na kasar Saudiyya ya shiga tasku, ko bacci baya iya yi saboda yunkurin yi mai juyin milki

Yarima mai jiran gado na Saudiyya,Muhammad Bin Salman ya kasa samun sukuni,sakamakon kin yi masa mubaya'a da 'ya 'yan tsaffin sarakuna suka yi,wanda hakan ke nuni da cewa za su iya hambarar da mulkinsa.


Tactical Report,wacce kafa ce ta yi fice haikan kan lamurran da suka jibanci makamashi da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya ta fallasa wannan sirrin da ya shafi masarautar Saudiyya,inda ta ce hankalin Bin Salman a tashe yake a kulli yaumin,sabili da yadda wasu 'yan ahlin Sa'ud ke gasa masa aya a hannu.

Wasu makusantan masarauta sun tabbatar da cewa,Bin Salman na fargabar kulle-kullen da yarimomin Saudiyya da ke ketare kan iya yi masa,musamman ma Abdel Aziz Bin Abdallah,da ga tsohon sarkin Saudiyya Abdallah ben Abdel Aziz kana mataimakin ministan harkokin wajen kasar a yau.

Saudiyya ta aika wa yariman Abdel Aziz Bin Abdallah goron gayyata sau tarin yawa don ya dawo gida, amma ya ki.

Yarima Abdallah ben Khaled ben Abdel Aziz ma, ya kasance daya daga cikin yarimomin da ake kyautata zaton cewa ba za a taba bar su a baya ba wajen kulla wa Bin Salman gadar zare.Baya ga haka akwai wasu karin yarimomi wadanda ke garkame ko kuma ke rayuwa a kasashen waje,wadanda suka hana yarima mai jiran gado rumtsawa.

Dukannin wadannan yarimomin sun ki wa Muhammed Bin Salman Mubaya'a.

Abinda yasa ahlin Sa'ud suka gudanar da wani taron sirri don jinkirta mallaka wa yariman mulkin kasar ga baki dayanta.

An rawaito cewa, akwai yiwuwar a nada kanen Bin Salman, Khaled Ben Salman,wanda a yanzu haka shi ne jakadan Saudiyya a birnin Washington DC na Amurka, a matsayin mataimakin yarima mai jiran gado.

Kafar Intelligence Online ta tabbatar sahihancin wannan labarin,inda ta kara da cewa, tuni yarima Khaled ya fara shirin karbar wannan mukamin.

Nada shi a matsayin yarima mai jiran gado ke wuya, Muhammad Bin Salman ya soke mukamin mataimakin yarima.

Kafar ta kara cewa, matakin da aka dauka na nada Khaled ben Salman a matsayin mataimakin yayansa Muhammad Bin Salman,zai sa ahlin sarki Salman ci gaba da rike akalar mulki a Saudiyya,idan har tsare-tsaren yarima mai jiran gado basu bille ba.

Hawan Muhammad Bin Salman kan karagar mulki ya haifar da tashe-tashen hankula tsakanin 'yan ahlin Sa'ud,abinda yasa aka garkame da yawa da cikin su don toshe bakunansu.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment