Monday, 20 August 2018

Yau Mahajjatan Bana Suke Hawan Arafat A Saudiyya

Kimanin alhazai kamar miliyan daya da rabi zuwa miliyan biyu ake kyatata zaton suke aikin hajjin bana a kasa mai starki, Saudiyya.


Wakilin Sashen Hausa dake Saudiyya Abdulwaba Muhammad, ya tabbatar da adadin mhajjjatan bana a kasa mai tsarki.

Sai dai a wannan lokacin, wani abun da ba saban yake faruwa ya auku. An yi ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi a birnin Makka. Saboda tsananin ruwa da iska sai da aka dakatar da wasu abubuwa a masallacin Makka. Baicin hakan, ruwan ya kawar da wasu abubuwa da dama kamar gidaje da bishiyoyi, lamarin da ya shafi harkar saye da sayarwa. Iskar ta yi fatali da wasu kayayyakin da aka kasa domin sayarwa.

Dangane da shirin hawan arfa, tun misalin karfe goma na daren Nigeria jiya Lahadi aka fara kai mahajjatan. Dangane da tsaro mahukuntan kasar sun girke jami'ansu walau a masallatai ko kan hanyoyi ko kuma wuraren da jama'a suke taruwa.

Gameda mahajjata daga Nigeria kowace jiha tana iyakar kokarinta, wajen jigilar alhazansu zuwa wuraren da suka kamata cikin motocin safa safa.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment