Friday, 17 August 2018

Yaushe Shugaba Buhari zai koma Najeriya?

Fadar Shugaban Najeriya ta ce sai ranar Asabar shugaban kasar zai koma gida bayan kammala hutun aiki da ya dauka.


Shugaban ya tafi birnin Landan ne domin hutun kwana 10, da ya fara a ranar 3 ga watan Agusta.

A farkon wannan makon ne wasu jaridun kasar suka bayyana cewa shugaban ya dage ranar da zai koma Najeriya, inda zai wuce kwanaki goma kamar yadda aka bayyana tun da farko.
To sai dai fadar shugaban ta musanta rahotannin.

Mai taimakawa shugaban na musamman kan yada labarai Malam Garba Shehu ya shida wa BBC cewa a ranar Asabar shugaban zai koma gida.

Garba Shehu ya ce Buhari zai yi kwanaki goma ne da ake aiki a cikinsu, don haka ba za a lissafa da Asabar da Lahadi da ke cikin makonnin da ya yi hutun ba a lissafi.

A bara dai Shugaba Buhari ya shafe watanni yana hutu a birnin Landan, abin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar.

Shugaba Buhari mai shekara 76 zai sake tsaya takarar neman shugabancin kasar a zabukan da za a yi a watan Fabrairun badi.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment