Sunday, 19 August 2018

Yi Wa Shugaba Buhari Addu'a Babban Jihadi Ne, Sakon Gwamnan Bauchi M.A Abubakar Ga Mahajjatan Nijeriya

Gwamnan Jihar Bauchi M. A Abubakar ya yi kira ga Alhazan Nijeriya da su shigar da Shugaba Buhari cikin addu'o'insu yayin gudanar da ayyukan hajjin bana. 


"Ina kira da babbar murya ga mahajjatan mu, da su dukufa wajen yi wa shugaba Muhammadu Buhari addu'ar samun nasara a duk wani aiki da ya tunkara, da kuma addu'ar samun nasara a zaben Shekarar 2019 domin kara bunkasar ayyukan alkairi da yake yi a duk fadin kasa". 

"Ku sani kasar mu na cikin wani hali, lokacin da Shugaba Buhari ya karbi mulki, ana kashe-kashe a ko ina. Amma zuwan Buhari an samu saukin haka. Na yi imanin Buhari ba azzalumi bane, wallahi na yi imanin Buhari ba barawo bane, kamar yadda na yi imanin cewa Nijeriya ba ta taba samun mutum mai gaskiya kamar shi ba".

Gwamnan ya ci gaba da cewa "Allah shine ya zaba mana shi domin ya gyara kasar, to idan muka yi watsi da zabin Allah tamkar munyi butulci ne gare shi. Ina rokon ku daku saka Buhari a cikin addu'ar samun nasara a zaben 2019. Idan har Buhari ya kara samun nasara, to hakika Nigeria zata gyaru na har abada Insha Allahu". Nagode.
Rariya.

No comments:

Post a Comment