Wednesday, 15 August 2018

Yin jima'i akai-akai yana kara tsawon rai

Shugaban kungiyar masu hankoron tsarin iyali, Dr. Ejike Orji, ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN cewa, masoya dake jima'i akai-akai sun fi wanda basa yi lafiya da tsawon rayuwa.


Yace wani bincike da akayi a Landan ya tabbatar da hakan. yin jima'i a kalla, sau biyu a sati yana sawa masu yi su samu karin lafiya, kariya daga ciwuka irinsu ciwon zuciya da tsawon rai fiye da wadanda basayi.

Ya kara da cewa, yin jima'i akai-akai yana sa mutum ya zama kamar matashi dan haka yayi kira ga masoya da su rika yin jima'ai akai-akai dan samun tsawon rai da karin lafiya,kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment