Wednesday, 12 September 2018

A tarihin Najeriya Ba'a taba yin shugaban da bai iya aiki ba irin Buhari>>Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma me neman takarar shugbancin kasarnan a zaben shekarar 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya mayarwa da shugaba Buhari martani akan kiran wadanda suka fita daga APC masu rauni da yayi a jiya lokacin da yake karbar Fom din takarar da aka sai mishi.


Atiku yace tunda aka kafa Najeriya ba'a taba samun shugaban kasa da baisan aikinshi ba da kuma ya tara mutanen da basu iya aiki ba kamar shugaba Buhari, ya kara da cewa, ai alamar rauni ta kare a gurin Buharin tunda shine ya kasa rike muhimman mutane a APC din, ya barsu suna ta canja sheka.

Ya kara da cewa, irin kwamacalar da Buharin yayi ne a mulkinshi yasa Atikun neman takarar shugaban kasa dan ya gyara, raba kawunan 'yan kasa da daidaita Najeriya ta yanda har ta kai an saka ta cikin kasashe mafiya talauci a Najeriya ne abinda Buhari yawa kasarnan.


No comments:

Post a Comment