Thursday, 6 September 2018

Abin dariyane wai ace Saraki na neman fitowa takarar shugaban kasa>>Inji APC

Jam'iyyar APC ta caccaki kakakin majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki akan fitowa takarar shugaban kasa da ya bayyana cewa zai iyayi, APC tace wannan magana ta Saraki abin dariyace.


Jam'iyyar ta bayyana hakne ta hannun me magana da yawunta, Yekini Nabina kamar yanda jaridar Punch ta bayyana, APC ta kara da cewa, idan aka lura da yanda Sarki yayi gwamnan jihar kwara sau biyu da kuma sanata na tsawon shekaru 3 amma be tsinanawa jihar tashi wani abin a zo a gani ba to za'a iya fahimtar cewa, shi ba mutum bane da ya dace da zama shugaban kasa ba domin idan aka bashi dama irin yanda yayi a Kwara zaiwa Najeriya.

Ta kara da cewa koda gwamnatin yanzu dake mulki wadda Sarakin ke kane-kane a harkar gudanar da mulkinta duk da cewa ba shine gwamna ba bata yi wani abin a zo a gani ba saidai azurta wasu mutane kawai.

No comments:

Post a Comment