Monday, 10 September 2018

Abinda fadar shugaban kasa ta fada na cewa babu maganar sayen motocin Hilux a kasafin kudi ba gaskiya bane: An gano gaskiyar lamarin

An gano cewa babu kanshin gaskiya a ikirarin da fadar shugaban kasa ta yi na cewa, babu maganar sayen motoci kirar Hilux a cikin kasafin kudin 2017 a kokarin da take na kare shugaban ma'ikata, Abba kyari da cewa ya karbi cin hanci dan baiwa wani dan kwagila kwangilar kawo motocin.


A sanarwar da me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Asabar din data gabata, inda yake mayar da martani akan zargin da akawa Abba Kyarin na karbar cin hancin Naira Miliyan 29 dan bayar da kwangilar sayen motocin, yace zargin karyane, babu ma maganar sayen Hilux a kasafin kudin shekarar 2017, ta yaya Abba Kyari zai bayar da kwangilar da babu ita a zahiri?

Saidai wani bincike da wata kungiyar kasa da kasa dake bincike da kawo rahotanni dan samar da kyakkyawan shugabanci, ICIR tayi tace ta gano cewa ikirarin da gwamnatin tayi ba gaskiya bane, dan kuwa akwai maganar sayen motocin Hilux a cikin kasafin kudin na shekarar 2017.


Kafar ta wallafa hotunan data dauka na kasafin kudin daidai inda ake bayanin sayen motocin.

Ta kuma kara da cewa, ta tuntubi Abba Kyari akan wannan batu dan ya mata bayani saidai yace, maganar sayen motocin Hilux guda 15 da akace an bayar da kwangilarsu yake so a nuna mishi inda aka fadi haka a kasafin kudin.

No comments:

Post a Comment