Saturday, 29 September 2018

Abinda tun tuni ya kamata ace kungiyar kwadago ta yiwa ma'aikata

Wadannan bayanai da zan kawo su ne ya kamata Kungiyar NLC tayi wanda zai fi amfanar da ma'aikatan da 'yan Najeriya.

1. Babu shakka ma'aikata suna bukatar a kara masu albashi, amma ya kamata NLC su matsa wajen ganin ana biyan ma'aikatan Najeriya albashinsu yadda ya kamata. Gwamnatin tarayya ce kawai da wasu jihohi ke iya biyan albashi yadda ya kamata a Najeriya.


2. Ana samun tsaiko wajen biyan fansho da tsaiko idan ma ba a ki biya ba. Duk da cewa dan abun da ake bayarwa bai taka kara ya karya ba ga ma'aikaci bayan ya bar aiki. Ni na ga wani darakta da ya bar aiki a wata ma'aikata na gwamnati amma ya kasa sayan ragon sallah saboda ba a biya shi hakkinsa ba na tsawon wata 11 bayan ya bar aiki.

3. Bambanci A Daukar Aiki. Yaran manya ne kawai suke samun aiki. A yanzu aikin gwamnati an warewa 'ya'yan 'yan siyasa ne da manya wadanda a batun gaskiya ba su bukatar aiki. Ina dalilin da zai sa 'ya'yan gwamnoni da ministoci da ma'aikatan shugaban kasa da sarakuna su mamaye ayyukan talaka? A batun gaskiya suna bukatar aiki? Amma shugabannin NLC suna duba wani abu daban.

4. Fifikon albashi a tsakanin wasu ma'aikatun gwamnati. Me ya sa NNPC, CBN, FIRS, NPA suke daukan ninki 300% kan sauran ma'aikata da suke sauran ma'aikatu daban?

5. Biyan Haraji: Komin kankantar ma'aikaci da yake karban albashi yana biyan haraji bayan harajin VAT da yake biya wajen siyan abinci da man fetur a kasuwa.

6. Samar da abubuwan jin dadin rayuwa cikin sauki kamar harkar sufuri da gidaje da ilimi da lafiya da ruwa da wutar lantarki da tsaro da hanyoyo.

Wadannan nan abubuwan sun fi matukar muhimmanci da su nema ba karin albashi ba wanda karin zai zama ba shi da wani amfani kwata-kwata.
Nishadi TV.

No comments:

Post a Comment