Thursday, 6 September 2018

Adam A. Zango ya durkusa gwiwoyi biyu gaban Ali Nuhu yana tuba

Ga dukkan alamu dai rikicin Adam A. Zango da Ali Nuhu ya zo karshe, bayan da suka kwashe tsawon lokaci basa ga maciji, a kwanannan ne Adam A. Zango ya yiwa Ali Nuhu mubaya'a akan cewa ya yarda shine sarkin kannywood bayan da ya saka hoton Alin ya kuma kirashi da sarki.Adamu ya kuma fada cewa, me guri ya dawo me a wani rubutu da yayi a kwanannan.

A wani lamari da ba'a zataba, Adamu ya sake kwantar da kai ya saka wannan hoton da ake gani a sama da yake tsugune a gaban Ali Nuhu sannan ya rubuta cewa, Tuba Nake Sarki, Gwiwowi na a kasa!!

Da dama sunyi mamakin wannan abu inda wasu ke tambayar anya ba kutse akawa shafin Instagram na Adamun ba? Saidai ga dukkan alamu Adamun ne da kanshi yayi wannan bayani.

Wannan na alamta cewa, ta bangaren Adamun ya sauko akan rikicin nasu da Ali Nuhu.

Zuwa yanzu dai Ali Nuhun be bayyana komai ba ta dandalinshi na sada zumunta akan wannan lamari.

No comments:

Post a Comment