Saturday, 29 September 2018

Ahmed Musa ya yabawa mahaifiyarshi

Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya yabawa mahaifiyarshi bisa irin gudummuwar da ta bashi a rayuwarshi inda yace ita tayi sanadin zuwanshi Duniya kuma a kullun take karfafa mishi gwiwa akan duk wani abu da yake yi.A cikin wani sako da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta, Musa ya kara da cewa, a duk lokacin da yayi tuntube a rayuwarshi itace ke tashinshi sannan ta karfafeshi, a karshe yace yana matukar godiya a gareta.

No comments:

Post a Comment