Wednesday, 26 September 2018

Ahmed Musa ya zama gwarzon dan wasan kasar Saudiyya hadi da kyautar kudi masu tsoka

Tauraron dan kwallon kafar Najeriya da ke bugawa kungiyar Alnassr ta kasar Saudi Arabia wasa, Ahmed Musa ya zama gwarzon dan wasan gasar kwallon kafa ta kwararru na kasar Saudiyyar bayan da ya ciwa kungiyarshi ta Alnassr kwallaye uku a wasa da ya.


Musa yaci kwallayenne a wasan da Alnassr ta buga da kungiyar Al Quadisiya a Ranar Laraba hakan yasa ya samu wannan karramawa hadi da kyautar kudi masu tsoka.

Musa ya godewa masoyanshi da suka zabeshi har ya kai ga samun wannan kyauta ta dandalinshi na sada zumunta inda yace ya gode da goyon bayan da suka nuna mishi.

No comments:

Post a Comment