Wednesday, 26 September 2018

Akwai damuwa: ‘Yan majalisar dokoki 9 a jihar APC sun fita daga jam’iyyar

‘Yan majalisar dokokin jihar Oyo 9 sun canja sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta ADC. Daga cikin mambobin da suka fita daga APC din har da mataimakin shugaban majalisar, Honarabul Abdulwasi Musah.


Magatakardar majalisar dokokin jihar Oyo, Paul Bankole, ne ya karanta wasikar canjin ‘yan majalisar yayin zamansu nay au, Talata.

Bayan mataimakin shugaban majalisar, daga cikin wadanda suka canja shekar akwai, Lukman Balogun, Bolaji Badmus, Azeez Billiaminu, Ganiyu Oseni, Olusegun Olaleye, Samson Oguntade da Muideen Olagunju.

Yanzu haka jam’iyyar ADC na da mambobi 12 a majalisar ta jihar Oyo yayin da jam’iyyar APC dake mulkin jihar keda mambobi 18. Jam’iyyar PDP na da mambobi 2 kacal a majalisar.

Jam’iyyar ADC na samun Karin karfi a jihar saboda canjin shekar da mambobin APC da PDP ke yi zuwa cikinta.

A kwanakin baya-bayan nan ne wasu mambobin majalisar tarayya biyu daga jihar Oyo, Sanata Soji Akanbi da Honarabul Abiodun Awoleye, suka canja sheka daga APC zuwa ADC.

ADC na daga cikin sabbin jam’iyyu da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yiwa rajista cikin shekarar nan.

Ana zargin cewar tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo ne ya kirkiro jam’iyyar ADC bayan ya daina goyon bayan gwamnatin Buhari. Sai dai tsohon shugaban kasar ya musanta cewar shi mamba ne a jam’iyyar ta ADC.
Naija.ng.


No comments:

Post a Comment