Thursday, 13 September 2018

Akwai Damuwa:Okonjo Iweala ta fitar da Najeriya daga bashi amma yanzu Najeriyar ta sake tsunduma cikin wani gagarumin bashin>>Amina J. Muhammad

Tsohuwar ministar muhalli ta Najeriya kuma mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya, Amina J. Muhammad ta bayyana damuwa akan yanda bashin da Najeriya ke da shi yanzu yake nema ya sha kan kasar.


Amina ta yi bayanine a wani zaman hadaka tsakanin majalisar dinkin Duniya da kungiyar bada lamuni da Duniya, IMF, inda tace akwai damuwa sosai irin yanda bashin Najeriya yakai wani matsayi dake neman shan kan kasar bayan da tsohuwar ministar kudi, Ngozi Okonjo Iweala ta taka rawar gani wajan ganin an yafewa Najeriya bashin da ake binta a baya.

Tace koda yake matsalar ba akan Najeriya bane kawai, haddama sauran kasashe masu tasowa a Afrika.

Tace dan haka ana bukatar zama a duba wannan lamari dan samun daidaito.

A lokacin Okonjo na ministar kudi dai an yafewa Najeriya zunzurutun bashin da ake binta da ya kai dala miliyan dubu 18 dalilin haka yasa bashin da ake binta a kasashen waje ya koma dala miliyan dubu 3 kawai.

Amma yanzu bashin ya sake komawa dala miliyan dubu 73, kamar yanda kafar The cable ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment