Monday, 3 September 2018

Ali Nuhu da Adam A. Zango sun shirya

Taurarin fina-finan Hausa, Ali Nuhu da Adam A. Zango sun jima suna samun sabani a tsakaninsu, a kwanakin baya da abin yaso ya rincabe, saida aka kirasu garin Kano wasu manya a harkar ciki hadda shugaban tace fina-finai na jihar, Isma'ila Afakallahu suka shiryasu.


Duk da wancan shirin da aka musu amma sai aka kara samun sabani.

Tun daga wancan lokaci dai ba'a kara jin wani abu na zahiri ya hada su ba.

Duk da yake cewa Ali Nuhu ne akewa lakabi da Sarkin Kannywood shi kuma Adamu ana mai lakabi da Yarima amma a kwanakin baya har wata kungiya ta yunkuro zata nada Adam A. Zangon a matsayin sarkin masana'antar ta Kannywood Kuma wasu mabiyansu sukan yi sa' insa akan wanene sarki a tsakanin Alin da Adamu.

Yanzu dai alamu na nuna cewa, Adam A. Zango da Ali Nuhu sun daidaita tsakaninsu.

Adamun ne da kanshi ya saka hotunan Ali Nuhu inda ya kirashi da sarkin Kannywood sannan a wani rubutun da yayi na daban kuma ya sake cewa, karshen muna fukai, mai wuri ya dawo, Allah ina godiya da irin wannan jarabtar da ka yi min.
Wannan na alamta cewa fadan nasu yazo karshe muna fatan Allah yasa haka.

No comments:

Post a Comment