Tuesday, 25 September 2018

Ambaliyar ruwa ta lalata gonar me magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu

A damunar bana an samu ambaliyar ruwa a jihohi da dama na Najeriya da tayi sanadiyyar salwantar rayuka da dukiyoyin jama'a da dama. Jihar Jigawa na cikin jihohin da wannan ibtila'in ya afkawa inda hadda gonar me magana da yawun shugaban kasa ta shiga ciki.


Gonar Garba Shehu ta shinkafa na cikin wadda ambaliyar ruwa ta lalata a jihar ta Jigawa inda aka nunashi yana tsaye yana duba irin barnar da ambaliyar tamai yayin da yaje ran gadi.No comments:

Post a Comment