Sunday, 2 September 2018

Amurkawa na kyamar mulkin Trump

Sakamakon wani bincike da jaridar Washington Post ta yi tare da hadin gwiwar kafar yada labarai ta ABC ya nuna cewa, kashi 60 cikin dari na Amurkawa na kyamar mulkin Donald Trump.


Duk da cewa kawo yanzu Trump mai cika shekaru 2 ba da hawa kan karagar mulki, amma Amurkawa na ganin cewa, bai tabuka komai.

A binciken an yi wa jama'a tambaya kamar haka : "Shin ko kun gamsu da salon mulkin Donald Trump ?"

Yayin da kashin 60 cikin dari na wadanda suka halarci wannan binciken suka ce "A'a", kashi 36 cikin dari kuma, sun nuna gamsuwarsu.

Haka zalika, Amurka sun soki lamirin Trump kan ababen kunya da ya dinka yi.

Yawanci daga cikin su na ganin cewa, kamata ya yi Majalidar Dattijan Amurka ta yi kadaran kadahan wajen hambarar da shi daga mulki.

A gefe daya kuma kashi 63 cikin dari, na bukatar a zurfafa bincike kan rawar da Rasha ta taka a zaben shugaban kasar Amurka a shekarar 2016.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment