Sunday, 2 September 2018

An daura auren dan kasar Chinannan da budurwarshi 'yar Najeriya

A kwanakin bayane labarin wani farar fata dan kasar China da ya zo Najeriya, Arewa jihar Filato, ya musulunta ya kuma samu matar aure ya watsu a shafukan sada zumunta da muhawara na yanar gizo.Bayan hotunan dan kasar Chinar da masoyiyarshi da danginta sun watsu sai kuma da babbar Sallar da ta gabata mukaga hoton shi yayin da ya halarci Sallar Idi.

A yanzu kuma labarin auren masoyan biyune ya bayyana, kamar yanda Rariya ta ruwaito.

Hotunan na yanzu sun nuna masoyan cikin shagali irin na aure wanda akayi shi a zamanance hadda kek da dai sauran abubuwan shagali.

Muna fata Allah ya Albarkaci wannan aure nasu.

No comments:

Post a Comment