Wednesday, 26 September 2018

An gano buraguzan wani jirgin ruwa a kasan teku bayan shekaru 400

A gabar tekun kasar Beljiyom an gano buraguzan jirgin ruwa mai shekaru 400.


Labaran da sashen Turkanci na tashar BBC ya fitar na cewa, a tsakanin shekarun 1575-1625 jirgin ya kife a kan hanyarsa ta dawo wa daga Indiya.

Daga cikin wadanda suka gabatar da bincike Jorge Freire ya ce, sun gano jirgin a karkashin teku da zurfin mita 12.

Frire ya ce, wannan abu ne na tarihi wanda zai iya zama mafi muhimmanci a 'yan shekarun nan.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment