Saturday, 29 September 2018

An gano motar sojan da ya bata a karkashin ruwa

Rundunar sojojin Nijeriya ta gano motar Tsohon Manjo Janar Alkali da aka daina jin duriyarsa tun 3 ga Satumba, 2018.

An gano motar ne yau a wani kududdufi da ke yankin Gundumar Du a Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

Yau kimanin mako guda ke nan da Rundunar sojojin Nijeriya take janye ruwan kududdufin da zummar gano motar bayan bayanan sirrin da ta samu na cewa an jefa motar Manjo Janar Alkali a ciki.
Rariya.

No comments:

Post a Comment