Friday, 28 September 2018

An hana ministan Buhari tsayawa takarar gwamna saboda rashin takardar NYSC

Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC yaki tantance ministan sadarwa Adebayo Shittu dake son tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo saboda be cancantaba.


Kwamitin ya bayar da dalilin rashin takardar yin bautar kasa ta NYSC da ministan beda shi a matsayin abinda yasa aka hanashi tsayawa takarar gwamna Kamar yanda yake a sanarwar da ta fitar.

Shittu dai ya kammala karatun jami'a yana da shekaru 24 wanda ya kamata ace yayi bautar kasa amma sai baiyi ba.

No comments:

Post a Comment