Thursday, 27 September 2018

An hana musulmai yin sallah da ajiye gemu

A wani kauyen kasar India an hana musulmai yin sallar Jam'i da kuma ajiye gemu saboda zargin mutuwar wani dan saniya a hannun wani matashin musulmi na kauyen.


Jaridar Telegraph ta ruwaito cewa, matashin da ya aikata wancan laifi an koreshi daga garin sannan kuma ya jawa sauran musulman garin an hanasu yin sallar jam'i, saidai su yi a gida an kuma hanasu sakawa 'ya'yansu sunan musulmai.

Jaridar ta ruwaito wata kotu na cewa zata tuntubi mahukunta kauye dan daukar matakin da ya dace aka  wannan lamari.

Daya daga cikin musulman dake kauyen yace basu iya saka hula ko kuma ajiye gemu tunda wancan lamari ya faru sannan sai sunje wani gari me nisa suke samun yin sallah.


No comments:

Post a Comment