Tuesday, 11 September 2018

An kama mai kula da dandalin WhatsApp da matan aure a Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani mai kula da shafin WhatsApp, wato admin, da wasu matan aure bisa zargin yada labarin karya.


Kakakin 'yan sanda na jihar, SP Magaji Musa Majiya, ya shaida wa BBC cewa mutanen suna yada hoton wata matar aure ne tare da yi mata kagen cewa tana satar yara a birnin Kano.

Majiya ya ce matar, wacce ma'aikaciyar gwamnati ce, ta kai musu korafin cewa ana yada hotonta a WhatsApp da nufin bata mata suna, da kuma yunkurin jefa rayuwarta cikin hadari.

Ya ce daga nan ne suka fara bincike, abin da ya kai su ga kama mutum uku, namiji daya da mata biyu, kuma dukkan su masu aure ne.

Kakakin na 'yan sanda ya ce mutanen sun tabbatar musu cewa su ma sun samu hoton ne, don haka suka ci gaba da yada shi.

Mutanen da aka kama dai sun shaida wa 'yan sanda cewa ba su san matar ba, kuma ba su yi yunkurin tantance labarin ba gabanin su fara yada shi, don haka suna neman gafara, kamar yadda Majiya ya shaida wa BBC.

Tuni dai rundunar 'yan sandan ta yi holin mutanen ga 'yan jarida, to amma an bayar da belin su daga baya.

No comments:

Post a Comment