Saturday, 15 September 2018

An kama masu boyewa da sayar da kudin Naira

Hukumar 'yansandan jihar Imo sun kama mutane dake boye da kuma sayar da takardar kudi ta Naira a wani samame da suka kai jihar tare da hadin gwiwar jami'an tsaron farin kaya dana babban bankin Najeriya CBN.


Hukumar 'yansandan ta gurfanar da mutane 10 data kama a gaban kotun magistre ta jihar dan yi musu hukunci daidai da laifinsu.

Da yake nunawa manema labarai masu laifin, kwamishinan 'yansandan jihar, Dasuki Galadanchi ya bayyana cewa sun kama mutanennen bisa karya dokar babban bankin Najeriya da suka yi wadda ta hana boyewa da sayar da kudin Naira.

Kuma kudin da suka kama sun kai sama da Naira miliyan biyar, yace hukuncin wannan laifi shine wata shida a gidan yari ko biyan tarar dubu 50 ko kuma duka.

Yace mutane su lura, watsa kudi a gurin biki ko yin rubutu a kansu ko kuma mutsutstsukesu ko boyewa da sayarwa duk laifine da za'a iya hukunta mutum akai.
Punch.

No comments:

Post a Comment