Wednesday, 26 September 2018

An kama mutuminnan da yayi barazanar kashe Atiku da kuma yiwa matarshi da diyarshi fyade

'Yansanda sun kama mutuminnan da ya yi barazanar tarwatsa jirgin tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuma cewa zai yiwa matarshi da diyarshi fyade ya kuma kashesu.Mutumin dan shekaru 43 da haihuwa me suna, Augustus Akpan ya fitone daga jihar Akwa-Ibom dake kudancin Najeriya kuma an kamashine a kan hanyarshi ta tserewa zuwa Birnin Legas dan gujewa neman da 'yansanda suke mishi kamar yanda kakakin rundunar 'yansanda ta kasa Jimoh Moshood ya bayyanawa manema labarai kamar yanda jaridar the nation ta ruwaito.

Mutumin yayi amfani da wayar satane yayi wancan barazana sannan ya amsa laifinshi, an kuma sameshi da laifin yaudarar wasu manyan mutane a kasarnan makudan kudaden Najeriya da na kasar waje, mutumin ya iya yaruka kamar su turanci, da yaren kasar Portugal dana Rasha da Ibibiyo.

Yace yayi kokarin amfarar iyalan Atikun kune ne sai baiyi nasara ba shiyasa ya buge da musu barazana kuma bashi da alaka da wani dan siyasa.

Hukumar 'yansanda tace da zarar ta kammala bincike zata tasa keyarshi zuwa kotu.


No comments:

Post a Comment