Tuesday, 4 September 2018

An mayarwa wani mutum kudin daya baiwa Buhari na yakin zaben 2015

Muhammad Abdullahi Baba ya fito yana kuka inda yace ina ma ace a maida masa kudin sa da ya kashe wajen yi wa Buhari da Jam’iyyar APC kamfe a baya. Allah ya nufa kuma ya dace inda ya samu wani ya biya masa bukatar sa.


Daga cikin wannan bayani na Muhammad Abdullahi Baba a shafin sadarwa na zamani na Tuwita, sai wani Bawan Allah mai suna Ahmad Arkindhele ya tuntube sa domin ya maida masa kudin da yace ya kashewa jirgin yakin Buhari.

Abdullahi Baba yayi ikirarin cewa ya sa kudin sa har N2000 a asusun kamfen din Jam’iyyar APC lokacin da Janar Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo su ke neman takarar shugabancin kasar nan shekaru kimanin 3 da su ka wuce.

Ahmad Arkindhele ya aikawa wannan Bawan Allah da yayi da-na-sanin wannan aiki na sa kudin sa N2000 ta bankin sa na Diamond kuma ya tabbatar da cewa kudin sun shigo. Masoyan Shugaban kasa Buhari sun yabawa wannan mutumi.

Wani Bawan Allah shi kuma ya koka da duk wannan abin da ya faru yana mai yin tir da lamarin inda yace ina ma ace shi ma za a biya sa kudin da ya kashe wuri-na-gugar-wuri har N50000 domin ganin Muhammadu Buhari yayi nasara a zaben 2015.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment