Thursday, 6 September 2018

An samu girgizar kasa a Abuja

A jiya, mazau na babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana cewa sunji kasa na motsi a sassa daban daban na birnin, wannan dai shine karin farko da aka samu irin wannan lamari a Abujan.

Mazauna birnin da dama ne suka bayyana firgicinsu a dandalinsu na shafukan sada zumunta inda sukace sunji motsin kasar amma basu yi tunanin girgizar kasace ba.

Wasu kuma sunce basu ji komai ba.

An fara jin wannan motsin kasarne daga yankin Mpape dake Abuja.

No comments:

Post a Comment